✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace mai juna biyu a kusa da makarantar Sojoji a Kaduna

Muna kira ga gwamnati ta kawo mana dauki.

’Yan bindiga sun sace wata mata mai juna biyu a Unguwar Lema ta yankin Mando da ke daura da makarantar horar da kananan hafsoshin soji ta NDA a Jihar Kaduna.

’Yan bindigar sun yi awon gaba da wasu karin mutane 7 a lokacin da suka shiga gidaje 3 da misalin karfe 1 na dare ranar Lahadi a Mando.

Wasu mazauna unguwar sun ce sun tsorata, saboda haka sun kasa fitowa daga gidajensu a lokacin da suka ji motsin ‘yan bindigar, inda suka yi kira ga gwamnati ta kawo musu dauki.

Duk da cewa gwamnatin Jihar Kaduna ba ta ce uffan a kan lamarin ba, amma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, ya ce zai bincika don samun karin bayani a kan abin da ya auku.

Sai dai har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a ji daga gare shi ba.