✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace limami da mutum 10 a Suleja

’Yan bindigar sun yi garkuwa da wani limami da wasu mutum 10 daga gidajensu. 

’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 11 a unguwar Chaza da ke wajen garin Suleja a Jihar Neja.

Kakakin ’yan sandan Jihar Neja, CSP Sani Badarawa ya tabbatar da faruwar lamarin.

Mazauna sun shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun yi garkuwa da wani limami da wasu mutum 10 daga gidajensu.

Da suke bayani, mazauna garin na zargin dakatar da ayyukan ’yan sa-kai a garin ya ba wa maharan damar kai farmakin.