Akalla fasinjoji 10 ne da suka taso daga Jihar Taraba ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin Jootar da ke Karamar Hukumar Ukum a Jihar Benuwe.
Aminiya ta ruwaito yadda fasinjojin da ke cikin wata mota kirar Sharon ’yan bindigar suka tare su a yankin Jootar, tare da yin awon gaba da su.
- Yadda labaran karya suka kusa kashe min aure — Lai Mohammed
- Sojoji sun fitar da sunayen mutum 97 da suke nema a ruwa a jallo
Sai dai rahotanni sun bayyana wadanda aka sace masu sana’ar hannu ne ba dalibai ba, sabanin yadda wasu majiyoyi suka bayyana.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewar, ’yan bindiga dauke da muggan makamai ne suka tare motar, sannan suka yi awon gaba fasinjoji 10 zuwa cikin daji.
“Bas din Sharon ce. Sun dauke wayar direban. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 12 na ranar Juma’a. Abin da direban ya fada min kenan. Ya dauko su ne daga Takum a Taraba kuma lamarin ya faru ne kusa da yankin Jootar.”
Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Ukum, Ezra Nyiyongo ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Makurdi.
“Kamar yadda na samu labari, direban ya dauko su ne daga Wukari, a Jihar Taraba zai kai su Gboko. Daga Gboko za su zarce zuwa Akure don yin sana’o’insu. Ni ma na samu labarin ne kawai daga direban,” in ji shi.
Sai dai Shugaban Karamar Hukumar Ukum, Victor Iorzaa, ya ce ’yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin.
Amma Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Emmanuel Adesina, ya yi watsi da rahotannin cewar an sace wasu daliban makaranta a hanyar Benuwe, kazalika bai yi karin haske kan wannan lamarin ba.