Wasu ‘yan bindiga a Jihar Anambra sun sace Okechukwu Okoye, dan Majalisar Dokokin Jihar mai wakiltar mazabar gwamnan Jihar Charles Soludo.
- Luis Suárez zai bar Atletico Madrid a karshen kakar wasanni
- Karuwar ta’ammali da kwayoyi na da alaka da yajin aikin ASUU — Obaseki
Rundunar ‘yan sandan jihar, ta tabbatar da sace Okechukwu Okoye, wanda ya ke wakiltar mazabar Aguata ta 1 a Majalisar Dokokin Jihar ta Anambra.
Mista Okoye, wanda dan asalin kauyen Usofia ne ya shiga hannun ‘yan bindigar ne a ranar Lahadi.
Kakakin ‘yan sandan Jihar, Toochukwu Ikenga, ya tabbatar wa da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) faruwar lamarin, inda ya ce an gano motar da dan majalisar ya ke ciki a lokacin da aka sace shi.
Ikenga ya ce ‘yan sanda sun shiga farautar wadanda suka sace shi da zummar ceto shi daga hannunsu.
Ayyukan mahara ko ‘yan bindiga na ci gaba da kamari a jihar, baya ga ayyukan ‘yan awaren Biyafara da ke faruwa ba kakkautawa.