’Yan bindiga sun kai hari kan dalibai mata na Kwalejin Lafiya ta Tsafe da ke Jihar Zamfara inda suka kwashe guda 4 bayan halartar wani bikin aure.
Bayanai daga yankin sun ce ‘yan ta’addar sun kama wadannan dalibai ne lokacin da suke komawa Kauran-Namoda daga Birnin Magaji.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne bayan tare motocin da ke dauke da wadanda abin rutsa da su, inda suka kwashi matafiya 18, cikinsu har da daliban mata 4 da wasu ’yan mata 3 da kuma wani mutum guda.
Tuni hukumomin Kwalejin Kula da Lafiyar ta hannun shugabansu Yusuf Maradun ya tabbatar da aukuwar lamarin wanda ya ce ba’a cikin makarantar aka kwashi daliban ba.
Maradun ya ce lokacin da aka sace wadannan daliban makarantar na hutun karshen shekara.
Wani dan uwan daya daga cikin daliban ya ce ‘yan ta’addar sun bukaci fansar Naira miliyan 20 kafin sakin diyarsu.
Jihar Zamfara na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro musamman hare- hare da kuma garkuwa da jama’a domin karbar kudin fansa.