✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace basarake a Ondo

Majiya ta kusa da ahalin basaraken ta ce, sai da ’yan bindigar suka yi harbe-harbe kofar fadar suka shiga shiga sannan suka tafi da shi

’Yan bindiga sun sace basaraken Oso, Clement Olukotun, a yankin Ajowa-Akoko, cikin Karamar Hukumar Akoko ta Yamma a Jihar Ondo.

A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), da misalin karfe 10:15 na dare ranar Alhamis ’yan fashin suka dira gidan basaraken suka yi awon gaba da shi.

Wata majiya mai kusanci da ahalin basaraken ta ce, sai da ’yan bindigar suka yi harbe-harbe don razanarwa, kana suka lalata kofar shiga fadar suka shiga gidan.

Majiyar ta ce, tun da farko maharan sun bukaci a bude musu kofar shiga da lalama, rashin hakan ya sa suka sa bindiga suka fasa kofar.

Ta kara da cewa, har zuwa safiyar Juma’a babu wanda ’yan bindigar suka tuntunba daga ahalin sarkin.

Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Funmilayo Odunlami, ya tabbatar da faruwar hakan.

(NAN)