✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace basarake a Neja

“Maharan sun zo a kan babura dauke da muggan makamai, sanye da kakin sojoji”.

’Yan bindiga sun sace wani basarake kuma Dodo na Wawa da ke gundumar Wawa a Karamar Hukumar Borgu ta Jihar Neja, Dokta Mahmud Ahmed Aliyu.

Wata majiya a fadar basaraken ta shaida wa wakilin Aminiya cewa maharan dauke da muggan makamai sun kutsa kai cikin fadar ne da wajen misalin karfe 9:00 na safiyar ranar Asabar sannan suka sace shi.

“Sun zo kimanin su takwas a kan babura dauke da muggan makamai, sanye da kakin sojoji. Kuma shi kadai suka tafi da shi,” inji majiyar.

Ya kuma ce ya zuwa yanzu, masu garkuwar ba su tuntubi kowa kan batun biyan kudin fansa ba.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Neja, ASP Wasiu Abiodun ya tabbatar da kai harin.

Ya ce, “Ayarin jami’anmu da kuma ’yan kato-da-gora na yankin tuni suka shiga farautar mutanen don ganin an ceto shi, su kuma an kamo su.”