✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace amarya da angonta a Katsina

Baya ga sabbin ma’auratan akwai mutane da dama da aka sace.

’Yan bindiga sun yi awon gaba da wata amarya da angonta bayan kashe jami’an sa-kai biyu a wani hari da suka kai unguwar Shola da ke birnin Katsina.

BBC ya ruwaito mazauna unguwar na cewa ’yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 1 da minti 25 na daren Asabar, inda suka shafe tsawon sa’a guda su na harbe-harbe.

Sun shaida cewa ’yan sa-kai sun rasa rayukansu ne a kokarin hana garkuwa da ma’auranta, sannan an jikkata wasu daga cikinsu.

Rahotanni na cewa dole ta sanya masu aikin sa-kai janye jiki bayan sun fahimci cewa ’yan bindigar sun fi karfinsu.

Wani mazaunin unguwar ta Shola da ke cikin Katsina ya shaida wa BBCn cewa, ’yan bindigar sun shiga unguwar ne bisa babura dauke da bindigogi suna harbe-harbe.

Mutumin ya ce ’yan bindigar sun fasa wani gida ta baya suka shiga, lamarin dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu da jikkatar wasu biyun.

Ya kuma ce baya ga sabbin ma’auratan akwai mutane da dama da aka sace, sai dai bai san adadi ba.

Wannan dai ba shi ne karon farko da mahara ke aukawa unguwar Shola ba, ko fiye da wata guda ma ’yan bindiga sun shiga yankin.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar wannan hari, inda ya ce jami’ansu sun dukufa don kubutar da amarya da angon.

SP Gambo ya kuma ce sun kubutar da wasu mutum shida da aka yi garkuwa da su a kauyen Tandama cikin Karamar Hukumar Danja, bayan wani samame da suka kai maboyar ’yan bidiga.

Kazalika, ya ce a yankin Karamar Hukumar Safana ma, sun yi nasarar kashe wani kasurgumin dan fashin daji mai suna Albdulkarim Faca-Faca da mutanansa bakwai a karshen mako, bayan barin wutar da wani jirgin yaki ya yi akan maboyarsu.