Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, ya koka cewa masarautarsa na fama da mamayar ’yan bindiga.
Sarkin Zazzau ya ce al’ummarsa na fuskantar barazanar masu garkuwa da mutane, lamarin da ya sa ba a barci da ido biyu a yankin Zariya da kewaye.
“Nan Zariya ba mu taba sanin irin wadannan fitintinu ba. Yanzu haka akwai hakiman da idan na gan su ma sai in ji gabana ya fadi, saboda ka san wani abu ma ya faru a kasashensu.
“Barci ba sa iya yi, yaransu ba sa iya zuwa makaranta; Kullum haka za a wuce da bindiga kamar ana wurin yaki, ba ka da yadda za ka yi.
“Hakimin ga shi, ya zo nan fashewa ya yi da kuka, a zuwan da yi a baya, duk jikinmu ya tsinke,” inji Sarkin a safiyar Litinin.
Da yake neman jami’an tsaro su kara kaimi wajen kare al’ummarsa, Sarkin Zazzau, ya ci gaba da cewa, “Mu yanzu yaki ne ya ci mu har gida. Kuma yanzu in za a je asibiti a dauke likita da iyalansa, to kuma ina ya rage.
“Dutsen Abba, garin gaba daya aka tasa, kowa ya fita gidanshi cikin dare; Hakimin an dauke ’ya’yansa uku, an dauke mata da wurin mutu 11.
“Washegari kuma aka shi kwalejin kimiyya da fasaha, kowa ya ga wannan a duniya. Washegari kuma aka shiga asibiti.”
Ya yi bayanin ne a yayin karbar bakuncin Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, tare da wasu shugabannin tsaro na Jihar, da suka kai masa ziyara domin jajantawa kan garkuwa da mutane da aka yi a Zariya a kwana-kwanan nan.
Sarki Ahmad Bamalli ya ce duk da yawan cibiyoyin tsaro da barikin sojoji da ke Zariya da sauran yankunan Masarautar Zazzau, al’ummar yankin na cikin zullumin yiwuwar harin ’yan bindiga.
Ya ce hakan babban abin takaici ne, sannan ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauki matakan da suka dace na kare al’ummar yankin da ma Jihar baki daya.
Da yake mayar da jawabi, Kwamishinan tsaron ya ba wa Sarkin Zazzau tabbaci cewa Gwamnatin Jihar Kaduna na yin duk abin da ya kamata na ganin cewa an samu tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar.