Wasu ’yan bindiga sun kwace babbar mota makare da kayan abinci a titin Gusau zuwa Magami da ke Karamar Hukumar Gusau a Jihar Zamfara.
’Yan bindigar dai sun tare motar ne da fari, inda suka umarce shi da ya shigar da ita daji.
- Ya maka Hadiza Gaban a gaban kotu saboda ta ki auren shi
- NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Bindiga Suka Hallaka Mutane A Coci A Jihar Ondo
Jim kadan bayan hakan ‘yan sandan da ke Magami suka samu labari, kuma take suka iso wurin aka yi musayar wuta da su da ‘yan bindigar.
Jami’an dai sun samu nasara kan ‘yan bindigar inda dole suka kyale babbar motar suka gudu.
Sai dai kamar yadda wani ganau mai suna Babangida ya bayyana mana, sun debi kadan daga kayan abincin da motar ta dakko.
Jami’an sun ceto direban motar, da kuma baburan da ‘yan bindigar suka gudu suka bari.
Mazauna yankin dai sun bayyana mana cewa titin mai nisan kilomita 50 ya zamo tarkon mutuwa ga matafiya, domin kuwa kullum sai an yi kisa ko garkuwa da masu binsa.
Haka kuma sun yi kira ga gwamnati da ta taimaka ta cece su daga hannaun ‘yan bindigar, domin acewarsu sun hana su noma a gonakinsu.
“Ba mai iya zuwa gonarsa yanzu, ko ranar Lahadin da ta gabata sun harbe wani manomi mai shekara 80 yayin da yake aiki a gonarsa.
“Ko yau ma mun ga manoma sun gudo zuwa birni bayan ‘yan bindigar sun yi kokarin far musu. Yanzu fa fiye da mutum 1,000 sun yi kaura daga nan saboda rashin tsaron da ya ta’azzara” inji wani manomi mai suna Sani Abubakar.
Mun tuntubi Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jJhar SP Muhammad Shehu, inda ya ce mu ba shi lokaci kan ya ce komai kan lamarin.