Mazauna kauyukan Kwapre da Dabna na Karamar Hukumar Hong a Jihar Adamawa sun rika barin gidajensu don neman mafaka saboda yawaitar hare-haren ’yan bindiga a yankin.
Kwapre da Dabna da Lar da Zah da kuma wasu kauyukan na cikin gundumar Garaha ne, inda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da babban sojan nan da aka kashe kwanakin baya, Birgediya Janar Dzarma Zurkusu, suka fito.
- An sace dan sandan da ke sashen yaki da garkuwa da mutane a Adamawa
- Mota cike da fasinjoji ta fada katuwar kwata a Legas
A cewar wani shugaban al’umma a yankin na Garaha, Hon. Hyella, mutane sun gudu daga Kwapre don su tsira da rayukansu.
“Yanzu haka, mutum bakwai ne kacal suka rage a kauyen Kwapre, dukkan ragowar sun gudu sun koma ko dai Hong ko Pella.
“Mutane suna da dalilansu na guduwa, saboda a watan Afrilu, mutum 52 aka sace a garin, amma har yanzu takwas ne kawai suka dawo.
“Yanzu da ta tabbata ’yan bindiga sun kafa sansani a yankin, dole mutane su gudu.
“Kullum sai an yi garkuwa da mutane, kuma ’yan bindiga sun ma fara sa wa mutane haraji,” inji shi.
Wata majiya a yankin da ta nemi a sakaya sunanta ta ce, “Mutanen Dabna yanzu sun yi kaura zuwa Gombi da kuma Hong, ’yan gidaje kadan ne yanzu a garin da ba su wuce 10 ba.”
Kakakin ’yan sandan Jihar ta Adamawa, DSP Suleiman Nguroje, ya tabbatar da lamarin, amma bai yi cikakken bayani a kai ba.
“Gaskiya ne akwai barazanar garkuwa da mutane a yankin. Hakika mutane suna da hujjar da za su tsorata. Amma Kwamishinan ’Yan Sanda, Ahmed Barde, ya ba da umarnin a tura da dakaru don kare yankin.