Wasu ‘yan bindiga sun kone Babbar Kotun Oguta da ke Karamar Hukumar Oguta a Jihar Imo.
Harin wanda ya faru a daren ranar Lahadi, na zuwa ne kasa da mako guda bayan da wasu ’yan bindiga suka kashe alkalin wata kotun majistare a jihar yayin da ake tsaka da zaman sauraron wata shari’a.
Aminiya ta gano cewar ‘yan bindigar sun mamaye harabar kotun da misalin karfe 11:30 na dare, inda suka yi wa ginin kotun ruwan harsashi.
Babbar kotun dai tana cikin harabar hedikwatar Karamar Hukumar da suka kai harin.
Wakilinmu ya samu labarin cewa, ofishin rajistara, ofishin daukar bayanan kara, dakin ajiye bayanai, ofishin alkalan babbar kotun da ofishin ma’aikatan kotun duk sun kone kurmus.
Shugaban Karamar Hukumar Oguta, Ofili Ijioma, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, ya ce an kai rahoton kone-konen ga jami’an tsaro.
Ya ce an fara bincike mai zurfi domin bankado wadanda ke da hannu a lamarin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Henry Okoye, ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani kan faruwar lamarin ba.