✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kone gidaje 30, shanu 100 da kayan abinci a Neja

Maharan sun farmaki yankin sau biyu a ranar Juma'ar da ta gabata.

Akalla gidaje sama da 30 da shanu 100 da kayan abinci ‘yan bindiga suka kone a unguwar Allawa da ke Karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja.

An ce Allawa na ɗaya daga cikin manyan yankuna da ake noma da ke manoma sama da 2,000 a yankin Lakpma na Karamar Hukumar Shiroro.

Shugaban kungiyar Allawa Youth Connect, Yusuf Musa, ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun mamaye yankin ne da misalin karfe 8 na daren ranar Lahadi.

Ya ce maharan sun kone akalla shanu 100 da babura 35 da buhun kayan abinci 150 da kuma gidaje sama da 30 a yayin harin.

Mazauna yankin sun koka kan yadda ba sa iya tafiyar kilomita daya ba tare da ‘yan bindiga sun farmake su ba.

Aminiya ta ruwaito yadda wasu ’yan bindiga suka kai wa al’ummar yankin hari da sanyin safiyar ranar Juma’a, inda suka kashe wani dan banga tare da yin awon gaba da mutum 12.

Mazauna yankin sun bayyana cewa, ’yan bindigar sun kai hari sau biyu a ranar Juma’a; daya da sanyin safiyar ranar da kuma wani da suka kai da daddare, amma dakarun soji suka fatattake su.

Harin ranar Lahadi, ya tilasta wa al’ummar yankin Pandogari da Kuta da kuma Gwada tserewa daga muhallansu sakamakon hare-haren ’yan bindiga.

Kokarin jin ta bakin sakataren yada labaran gwamnatin jihar, Bologi Ibrahim ya ci tura.

Kazalika, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, bai ce komai game da harin ba.

Jihar Neja na daya daga cikin jihohin Arewa da ke fama da hare-haren ’yan bindiga.