Mafarauta sun lalata wata katuwar gonar tabar wiwi da ake zargin mallakin ’yan bindiga ce.
Kwararrun mafarautan sun kuma cafke ’yan bindiga hudu a samamen da suka kai maboyar ’yan bindigar da ke yankin Osara na Karamar Hukumar Okehir ta Jihar Kogi.
Bincike ya gano cewa masu garkuwar sun horar da karnuka na musamman a dajin domin hana mutane shigowa wurin da gonar ta tabar wiwin take.
Mafarautan sun kashe 10 daga cikin karnunan, baya ga cafke hudu daga cikin ’yan bindigar da suka yi kaurin suna wajen yin garkuwa da mutane a kan babbar hanyar Lokoja zuwa Okene.
Da yake jagorantar aikin, Shugaban Karamar Hukumar Okehi, Hon. Abdulraheem Ohiare, ya ce Jihar Kogi ba za ta lamunci ayyukan bata-gari ba, don haka za ta ci gaba da fatattakar miyagun.
Ya yaba wa kokarin Gwamnan Jihar, Yahaya Bello na ganin cewa Jihar Kogi tana zaune cikin aminci.