’Yan bindiga sun yi wa tawagar jami’an tsaron dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Ifeanyi Okowa kwanton bauna tare da kashe ’yan sanda uku.
Rahotonni sun ce maharan sun far wa tawagar jami’an tsaron da suka hada da ’yan sanda hudu a daidai garin Ihiala da ke Karamar Hukumar Ihiala ta Jihar Anambra.
- Ba mu taba samun sojoji da zargin take hakkin dan Adam ba —Shehun Borno
- ISWAP ta kashe Kwamandan Boko Haram Abu Zara da mayakansa 15 a Borno
Wasu majiyoyi sun ce jami’an tsaron na kan hanyarsu ta zuwa Jihar Abia, inda aka tsara Mista Okowa zai je domin ganawa da wasu mambobin jam’iyyar PDP a jihar gabanin Babban Zaben kasar da ke tafe ranar 25 ga watan da muke ciki.
Rundunar ’yan sandan Jihar Anambra ta tabbatar da faruwar lamarin.
A jerin wasu sakonni da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Mista Okowa ya mika sakon ta’aziyyar gwamnatin jihar da iyalansa zuwa ga iyalan mamatan, wadanda ya bayyana a matsayin ‘jajirtattu’.
Mista Okowa wanda shi ne gwamnan Jihar Delta, ya yi addu’ar samun rahama a gare su, sannan kuma yi alkawarin nema wa iyalansa hakkinsu.