✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama jarkokin manja maƙare da alburusai a Abuja

Mutumin da aka kama ya ce an biya shi N100,000 domin karɓo alburusan daga wajen wani mutum a Jihar Nasarawa.

Rundunar ‘yan sandan Birnin Tarayya ta ce ta kama damin alburusai 488 da aka ɓoye a jarkar manja a tashar mota.

Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da ke kula da sintiri na musamman a Abuja, DCP Ishaku Sharu, ne ya bayyana hakan lokacin da yake holen wanda ake zargin a ofishin rundunar a ranar Litinin.

Ya ce rundunar ta samu nasarar kama wanda ake zargin ne bisa tallafin wasu jami’an ƙungiyar masu sufurin motocin haya (NURTW).

Kazalika, ya ce sun kama wanda ake zargin ne ɗan asalin Jihar Katsina, ɗauke da harsashi 488 na bindigogin AK-47 da ya ɓoye a jarkokin manja.

DCP ya ce bayan rutsa shi ne ya bayyana musu cewa wani Yakubu Kacalla ne ɗan garin Funtua da ke Katsinan ya biya shi N100,000 domin karɓo masa kayan daga wajen wani mutum a Jihar Nasarawa.

Yanzu haka dai wanda ake zargin na hannun ‘yan sanda inda suke ci gaba da bincike domin kamo sauran masu hannu a safarar makaman.