✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe ’yan kasuwa 4 a Katsina

Maharan sun yi wa ’yan kasuwar kwanton bauna a kan hanyarsu ta zuwa kasuwar mako-mako ta Jibiya.

Akalla ’yan kasuwa hudu ne ’yan bindiga suka hallaka har lahira a kauyen Zandam da ke Karamar Hukumar Jibiya ta Jihar Katsina.

Shugaban Karamar Hukumar Jibiya, Bashir Sabiu Maitan, ya shaida wa manema labarai cewa maharan sun kashe ’yan kasuwar ne a kan hanyarsu ta zuwa Kasuwar Jibiya da ke ci mako-mako a ranar Lahadi.

Wata majiya a kauyen Zandam, da ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa harin daukar fansa ne saboda, “Jiya (Asabar) wasu ’yan banga sun kashe wani Bafulatani, shi ne yau maharan suka kawo hari suka kashe mutum hudu a hanyar Kasuwar Jibiya.

“Mutum biyar suka harba, amma take hudu suka mutu, na biyar din, Malam Ibrahim Julius, yana asibiti yana jinya.”

Ko da aka tuntubi kakakin ’yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce wanda ya ji raunin yana kwance a Babban Asibitin Katsina.

Karamar Hukumar Jibiya na daga cikin yankunan da ke fama da hare-haren ’yan bindiga, lamarin da ya sanya gwamnatin jihar a baya-bayan nan ta bayar da umarnin rufe titin da ya tashi da Jibiya zuwa Zurmi a Jihar Zamfara.

%d bloggers like this: