’Yan bindiga sun kashe tsohon Kwamishinan Hukumar Kidaya da Kula da Yawan Al’umma ta Kasa wato NPC, Malam Zakari Umaru-Kigbu.
Bayanai sun ce lamarin ya auku ne da safiyar Lahadin nan a gidansa da ke Unguwar Azuba Bashayi a Karamar Hukumar Lafiya ta Jihar Nasarawa.
- Mun fi samun kayan aiki a lokacin Buhari – Babban Hafsan Sojin Kasa
- Malamin cocin da aka dakatar ya lashe zaben fid-da-gwanin APC a Binuwai
Wakilinmu ya ruwaito cewa, bayan kashe tsohon Kwamishinan, ‘yan bindigar sun yi awon gaba da ’ya’yansa mata biyu kamar yadda wani dan uwan marigayin da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar al’amarin.
Wasu majiyoyin kuma sun ce ‘yan ta’addan sun nemi a biya su naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa kafin sako mata biyun da suka sace.
Kazalika, Kakakin ’yan sandan Jihar, Rahman Nansel ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce “mun samu wani kira mai tayar da hankali da misalin karfe 12:20 na dare, nan da nan muka tashi jami’anmu da kuma sojoji domin zuwa shiyyar da abin ya faru.
“Da zuwansu suka ga an harbi mutumin a cikinsa. An garzaya da shi asibiti cikin gaggawa amma da zuwa likitoci suka ce ya riga ya mutu, a gefe daya kuma an sace ’ya’yansa mata biyu, ya zuwa yanzu kuma ba a san makomarsu ba.”
Ya kara da cewa jami’ansu sun baza komar neman wadanda suka aikata wannan mummunan laifi kuma da an kama su za su girbi abinda suka shuka.
Kafin rasuwarsa, Zakari Kigbu malami ne wanda ke koyarwa a kwalejin Isa Mustapha Agwai a Lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa.