✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe shugaban matasan Fulani a Filato

’yan bindigar sun same shi tare da kawunsa amma shi kadai suka yi ta harbi.

’Yan bindiga sun harbe Shugaban Matasan Kungiyar Ci Gaban Fulani ta ta Gan Allah (GAFDAN), a Karamar Hukumar Barikin Ladi da ke Jihar Filato.

Wanda aka kashe din, Alh. Ya’u Yusuf, danginsa sun ce an kai masa harin ne a daren ranar Alhamis yayin cin abinci a gaban gidansa da ke Barikin Ladi da misalin karfe 7 na dare.

Shugaban kungiyar GAFDAN na Jihar, Garba Abdullahi Muhammed, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun samu mamacin ne tare da kawunsa amma shi kadai suka yi ta harbi.

Ya ce, “Yana cin abinci tare da wani abokinsa a gaban gidansa sai, kwatsam yan bindiga suka bude masa wuta. Sun harbe shi sau da yawa.

“Baturen ’Yan Snada na Barikin Ladi ya ziyarci wurin da lamarin ya faru sannan suka dauke gawar suka ajiye a asibiti. Na kuma sanar da Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar game da lamarin,” inji shi.

Da aka tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sanda na jihar, Ubah Gabriel kan lamarin, amma bai amsa kiran wayar ba da kuma sakonnin tes da aka aike masa.