Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutum biyar da ’yan bindiga suka kashe a Kananan Hukumomin Chikun da Igabi.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Mista Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a ranar Asabar.
- Hatsarin jirgin ruwan Kebbi: Majalisa ta tallafa wa iyalai da N10m
- Sojan da ya kashe jami’in kwastam ya kashe kansa
Kamfanin Dillancin Labarai NAN ya ruwaito Aruwan yana cewa, ’yan bindigar sun kashe mutum biyu tare da kone gine-gine ciki har da wajen ibada a Karamar Hukumar Chikun.
Kazalika, ya ce an kashe mutum uku a yankin Lambar Zango da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya a Karamar Hukumar Igabi.
Aruwan ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana takaicinsa kan aukuwar lamarin tare da aike sakon ta’aziyya zuwa ga ’yan uwan wadanda suka rasu.