Aƙalla mutum bakwai ne suka rasu a wani sabon hari da ’yan bindiga suka kai a daren ranar Asabar ƙauyen Mai Dabino da ke ƙaramar hukumar Danmusa a Jihar Katsina.
Wani ganau a ƙauyen, ya ce maharan sun sace mutane da dama waɗanda ba a san adadinsu ba kawo yanzu.
- Abba ya umarci jami’an tsaro su kawo ƙarshen faɗan daba a Kano
- Mai laifin da ake nema ya zama kurman bogi na tsawon shekara 20
A cewarsa galibin waɗanda aka sace mata da ƙananan yara ne.
Kazalika, ya bayyana cewar cewa ’yan bindigar sun shafe tsawon sa’o’i uku suna taɓargaza a yankin tun misalin ƙarfe 10:00 na dare, inda suka yi harbi ba ƙaƙƙautawa.
Ya ce maharan sun ƙone wasu da ransu a yankin.
Maharan ɗauke da makamai sun kuma ƙone gidaje da dama, da shaguna da kuma motocin miliyoyin Naira.
Kakakin ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi.
A cewar ASP Sadiq, rundunar na gudanar da bincike, kuma za ta yi ƙarin haske kam harin.
“Jiya, 22 ga watan Yuni, 2024, da misalin ƙarfe 10 na dare, ‘yan bindiga ɗauke da muggan makamai, sun kai hari ƙauyen Maidabino da ke ƙaramar hukumar Danmusa, inda suka kashe mutum bakwai.
“A halin yanzu ana ci gaba da bincike, nan gaba za a yi ƙarin bayani,” in ji shi.