Mutum uku sun rasu a wanin hari da ’yan bindiga suka kai a kananan hukumomin Lere da Birnin Gwari a Jihar Kaduna.
Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya ce ’yan bindiga shida sanye da bakaken kaya da takunkumi sun kai hari a anguwar Warsa Piti da ke yankin Mariri a Karamar Hukumar Lere inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi.
- Barayi sun fasa ofishin Media Trust dake Kaduna
- Jami’an tsaro sun ceto mutane 4, sun cafke ‘yan bindiga 3 a Kaduna
- Gwamnatin Kaduna ta sanar da ranar sake bude makarantun sakandiren jihar
- ’Yan bindiga sun hallaka mai juna biyu a hanyar Kaduna
Sanarwar da Aruwan ya fitar ranar Talata ta ce bayan samun kiran neman agaji ne rundunar sojin ‘Operation Safe Heaven’ ta kai dauki yakin inda dakarim suka fatattaki maharan zuwa cikin daji.
Sai dai ya ce ’yan bindigar sun kashe mutum biyu a yayin artabun da suka yi da sojojin.
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta kuma samun rahoton harin ’yan bindiga a kauyen Randagi na Karamar Hukumar Birnin Gwari ta jihar.
“Mutum daya ya rasu, an jikkata wasu a harin sannan ’yan bindigar sun wawashe kaya a shagunan yankin,” cewar Aruwan.
Ya ce a nan ma sojoji sun fafari ’yan bindigar har cikin daji bayan da suka samu rahoton harin.
An kai wa Fulani Hari a Kaduna
Kwamishinan ya ce wasu matasa sun kai wa wata rugar Fulani hari a kauyen Kurmin Bi da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf.
Aruwan ya ce sakamakon haka Fulanin yankin sun tsere daga yankin, sai dai matasan sun kashe musu shanu shida tare da raunata wasu.
“An kone gida a rugar Fulanin yayin da matasan suka kai farmakin,’’ inji shi.
Ya ce gwamnan Jihar, Nasir El-Rufai ya bayyana damuwarsa game da farmakin, sannan ya yi wa wadanda suka rasu addu’ar samun rahamar Ubangiji.
El-Rufai ya kuma ba da tabbacin cewa jami’an tsaro za su ci gaba da ba wa yankin Birnin Gwari tsaro daga ta’addancin ’yan bindiga.