Ana fargabar cewa ’yan bindiga sun kashe mutum akalla 26 cikin wasu hare-hare da suka kai a kauyuka hudu na Jihar Filato a ranar Lahadi.
Maharan sun far wa kauyukan ne da ke Karamar Hukumar Kanam a kan babura, inda suka dinga harbe mutane tare da kona gidaje masu dimbin yawa da kuma sace shanu.
- Dalilin da muke son kwato Kano daga APC da PDP — Dokta Isyaku Rabi’u
- PRP za ta iya samar da wanda zai gaji Buhari — Falalu Bello
Mazauna yankin sun ce an ga gawar mutum 20 a garin Gyambau, sannan an ga wasu shida a Kyaram.
Kazalika, an kai hare-hare a garuruwan Dungur da Kukawa, inda mutane da dama suka bace kuma sakamakon harin.
Hukumomi sun ce an tura karin jami’an tsaro a yankin kamar yadda BBC ya ruwaito.
Jihar Filato ta sha fama da rikicie-rikice da ke da nasaba da kabilanci da kuma addini, kafin daga baya ’yan fashin daji masu kashe mutane da kuma garkuwa da su don neman kudin fansa su ta’azzara matsalar.