’Yan bindiga sun kashe akalla mutum 20 a Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.
Maharan sun rika banka wa gidaje da motoci da amfanin gona a gonaki wuta a wasu kauyuka uku.
- Turji: Kasurgumin dan bindigar da ya addabi Zamfara Na neman a yi sulhu
- Gobara ta kone shaguna da gidaje sama da 300 a kasuwar kayan gini a Legas
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da harin a ranar Lahadi.
Ya ce an kai hare-haren ne a kauyukan Kauran Fawa da Marke da kuma Riheya da ke yankin Idasu.
Aruwan ya bayyana ta’aziyyar Gwamnan Jihar, Nasir El-Rufai ga iyalan mamatan tare da umartar Hukumar Ba Da Agaji ta Jihar ta kai musu tallafi.