✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 2 sun sace 13 a Zamfara

Mako 3 ke nan bayan ’yan bindiga sun sace mata 23 da ma'aikata 10 na wani kamfanin gini a jihar.

’Yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da sace wasu 13 a kauyen Mayanchi da ke Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara.

An kai harin na ranar Litinin ne mako uku bayan ’yan bindiga sun sace wasu mata 23 a Karamar Hukumar Maradu, da kuma ma’aikata 10 na wani kamfanin gini a Karamar Hukumar Talata Mafara a jihar.

Wani mazaunin kauyen Mayanci ya ce ’yan bindigar sun kai harin ne da rana tsaka suna harbi, inda suka shiga gidan ma’ajin kungiyar ’yan jarida ta Najeriya (NUJ), Aminu Mayanci, suka yi awon gaba da ’ya’yansa maza guda uku.

“Sun harbi mutum daya bayan ya yi musu turjiya, sannan suka shiga masallaci inda wasu mutane ciki har da wani shugaban ’yan banga suka buya, suka yi awon gaba da su,” in ji shi.

Wakilinmu ya yi kokari amma ya kasa samun kakakin ’yan sandan jihar ASP Yazid Abubakar, game da wannan batu, saboda wayar jami’in tana kashe.