Wasu ’yan bindiga sun kashe mutane 19 tare da jikkata wasu da dama a ƙauyen Agojeju-Odo da ke Karamar Hukumar Omala ta Jihar Kogi ranar Alhamis.
Wani mazaunin unguwar ya yi zargin cewa fafatawar da aka yi tsakanin ƙungiyoyin ‘yan bindiga a wasu sassan Jihar Benuwe ne ya haddasa kai hare-hare a garuruwan Agojeju-Odo da Ajokpachi-Odo da Bagaji da kewaye.
“Sun lalata amfanin gona wanda wannan lamari zai jefa jama’ar yankin cikin rudani,” in ji shi.
Mai bai wa Gwamnan Kogi shawara kan harkar tsaro, Commodore Jerry Omodara mai ritaya, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a yayin zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a Lokoja.
Ya ce gwamnan ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
“Kisan mutanen 19 da ba su ji ba ba su gani ba abin takaici ne kuma ba za a amince da shi ba.
“Yanzu dai an samu zaman lafiya a yankin, bayan da aka tura jami’an tsaro, waɗanda ke sa ido a wurin,” inji shi.
Omodara ya ce, an lalata dukiya musamman gidaje, motoci, da amfanin gona a yayin harin.
Ya kuma yi kira ga jama’ar Agojeju-Odo da sauran al’ummomin da ke maƙwabtaka da su kwantar da hankalinsu domin gwamnati da jami’an tsaro ta tari hanzarin lamarin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, SP Williams Oɓye-Aya, shi ma ya tabbatar da faruwar harin tare da ba da tabbacin cewa jami’an tsaro na ci gaba da sa ido a kan al’umma domin daƙile abin da ka iya zuwa ya komo.