Wasu ’yan bindiga sama da 60 sun kai hari kauyen Baka da ke Karamar Hukumar Ardo-Kola a Jihar Taraba inda suka kashe mutane sama da 15.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, ’yan bindigar sun shigo kauyen ne daga kogon su da ke saman wani dutse da misalin karfe 7:30 na yammacin Juma’a inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.
Bayanai sun ce ‘yan bindigar sun kona gidaje baya ga satar shanu da wawushe kayayyaki a shaguna da gidajen mazauna kauyen.
Wani mazaunin garin, Yakubu Garba ya ce a lokacin da maharan suka zo galibi mazauna kauyen sun tafi sallar Juma’a.
Ya bayyana cewa wannan dalilin ne ya sanya aka dakatar da sallar kowa ya ranta a na kare wajen neman mafaka.
Yakubu Garba ya ce wasu mazauna garin sun tsere zuwa wani daji da ke kusa da su, yayin da wasu mutum biyu ‘yan gida daya na daga cikin wadanda aka kashe yayin harin.
Ya ce adadin wadanda aka kashe na iya karuwa saboda wasu mutane da dama sun tsere zuwa cikin dajin da raunukan bindiga.
Ya ce ya zuwa yanzu an tsinto gawarwaki fiye da goma amma har yanzu akwai mutanen da aka nema aka rasa ciki har da mata da yara.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Taraba, SP Usman Abdullahi ya tabbatar da faruwar harin, sai dai bai iya bayyana ainihin adadin wadanda suka mutu ba saboda a cewarsa ana ci gaba da jiran rahoton faruwar lamarin daga sashin ‘yan sandan yankin na Sunkani.