Kungiyar kare hakkin dan-Adam ta kasa da kasa, Amnesty International ta ce ’yan bindiga sun kasshe akalla mutum 1,126 a kauyukan Arewacin Najeriya cikin watanni shidan farkon wannan shekara.
Ta ce kashe-kashen sun faru ne a jihohin Kaduna, Katsina, Neja, Filato, Sokoto, Taraba da kuma Zamfara, tare da zargin sojojin Najeriya da gaza kare su a yayin da hare-haren kungiyar Boko Haram ke karuwa.
A sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, Amnesty ta zargi mahukunta da rura wutar kashe-kashe da satar jama’a saboda gaza gurfanarwa da kuma hukunta masu aikata laifukan.
Ta kuma ce tana da cikakkun rahotannin cin zarafin manoma da kungiyoyin kare hakkin dan-Adam da ke yin kira ga gwamnati ta dauki matakan da suka dace.
- Sabuwar dabarar da ’yan bindiga ke amfani da ita a Katsina
- Dole a shiga Sambisa kafin a gama da Boko Haram —Zulum
- IPOB ta debo ruwa dafa kanta —DSS
“Rashin yin katabus daga jami’an tsaro wajen kare rayukan jama’a daga wadannan hare-hare abun kunya ne matuka,” inji Darektanta Anmnesty a Najeriya, Osai Ojigho.
“Bugu da kari, jami’an tsaro na jan kafa wajen kai dauki ga jama’a bayan samun gargadi ko barazana daga mahara da kuma rashin hukunta wadanda aka kama ya sa ’yan kauyukan sun rasa madafa”, inji ta.
– Irin barnar da ’yan bindiga ke yi
Kungiyar ta yi zargin cewa yawanci maharan a kan babura dauke da muggan makamai kan yi wa kauyukan kawanya suna harbi kan mai uwa da wabi, su kona gidaje wuta, su sace dabbobi da amfanin gona da kuma mutane domin neman kudin fansa.
Ta ce akalla mutum 380 aka sace a jihohin Kaduna, Neja, Katsina, Nasarawa da Zamfara a 2020, yawancinsu mata da kananan yara.
Kazalika, ’yan bindigar kan kashe iyalan da suka gaza biyan kudaden fansar da aka yanka musu.
Amnesty ta ce akwai wani hari da aka kai Unguwar Magaji a Jihar Kaduna amma ko da jami’an tsaro suka je wajen, da suka ga makaman maharan sun fi nasu sai suka juya, kafin su dawo kuma an kashe kusan mutum 17.
A Jihar Taraba kuwa, kungiyar ta yi ce akalla mutum 77 rikicin kabilanci tsakanin kabilun Tibi da Jukun ya hallaka.
A ranar 28 ga watan Mayu kadai, a cewara, harin ’yan bindiga ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 74 a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto
A Katsina, rikicin ya yi sanadiyyar raba manoma da dama da gonakinsu da kuma iyalansu.
– Illar barnar maharan
Kimanin mutum 33,130 ne a wadannan jihohin yanzu suke zaune a sansanonin gudun hijira. Wasu kuma sun koma wurin ’yan uwa, yayin da dubban manoma kuma a bana ba za su iya noma gonakinsu ba.
Daga nan sai kungiyar ta yi kira ga mahukuntan Najeriya da su tashi tsaye wajen gudanar da bincike a kan kashe-kashen tare da hukunta wadanda duk aka samu da laifi.
– Hukumomi sun yi gum
To sai dai da aka tuntube shi a kan rahoton na Amnesty, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, Frank Mba ya ki cewa uffan.
Wannan ba shi ne karon farko da rahoton kungiyar ke zargi hukumomin Najeriya da gaza kare rayuka da dukiyoyin jama’a yayin wadannan hare-haren ba.
Ko da yake a mafi yawan lokuta hukumoin ksar kan musanta zarge-zargen kungiyar.