Akalla mutum 11 ne ’yan bindiga suka kashe, wasu 13 kuma suka jikkata bayan wani hari da ’yan bindiga suka kai gida-gida wasu yankunan Karamar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Gambo Isa ya ce, “A ranar Talata da misalin karfe 7:15 na dare, wani gungun ’yan bindiga dauke da bindigun AK-47 sun kai hari kauyukan Katoge da ’Yanturaku na Karamar Hukumar Batsari, inda suka kashe mutum 11, suka jikkata 13.
- Sabon ‘virus’ din wayoyi ya bulla a Najeriya —NCC
- ’Yan Najeriya 90,000 ne suka kamu da kwalara a bana
“Tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar ya tura Mataimakin Kwamishina mai kula da ayyauka na musamman da wasu karin jami’ai zuwa yankin, kuma an tsaurara matakan tsaro,” inji kakakin.
Aminiya ta kuma gano cewa yayin harin, ’yan bindigar sun kona kadarori da yawa a yankunan.
Sun kai hare-haren ne da yammacin ranar Talata, kuma sun shafe kusan sa’a biyu, sannan suka kona gwamman gidaje da gine-ginen gwamnati da motoci.
Shaidun gani da ido sun ce an fara kai harin ne a daren Talata, kuma ’yan bindigar sun kai har kusan farkon safiyar Laraba suna cin karensu ba babbaka.
“A dukkan kauyukan da aka kai harin, ’yan bindigar sun rika harbi a iska don ankarar da mutane shigowarsu, kafin su fara bi gida-gida suna satar kayayyaki suna cin zarafin mutane,” inji majiyar.
Akwai wani rade-radi da ake a yankin cewa daga daga cikin wadanda aka kashe din, har da wani lauya mai suna, Barista Nura Hassan Wagine, ko da yake Aminiya ba ta kai ga tantance sahihancin labarin ba.
Da wakilinmu ya tuntubi mamba mai wakiltar mazabar Batsari a Majalisar Dokokin Jihar, Hon. Jabir Yauyau, ya ce ya samu labarin kai harin, amma har yanzu yana ci gaba da tattara bayanai a kan hakikanin abin da ya faru.
Sai dai ya ce sakamakon yanke hanyoyin sadarwa a yankin, zai yi wahala a samu cikakkun bayanai yanzu.
“An shaida min kai harin da mutanen da aka kashe, galibinsu mutanen da na sani ne, amma duk da haka ina bukatar na kara tantancewa,” inji dan majalisar.