✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun sace 8 a Katsina

'Yan bindigar sun yi awon gaba da dabobbi mutumin da suka kashe.

’Yan bindiga sun kashe mutum daya tare da sace wasu takwas a yankin Karamar Hukumar Batsari a daren ranar Talata a Jihar Katsina.

Wata majiya a garin Batsari da ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa mutumin da ’yan bindigar suka kashe mai suna Malam Tasi’u, sun yi awon gaba da dabobbinsa.

“Sun zo cikin dare da misalin karfe 3 na dare suka sace shanunsa.

“Daga baya suka sake dawowa suka harbe shi har lahira.

“Yana sana’ar sayar da ganda ne, ko jiya da yamma muna tare da shi a nan,” cewar majiyar.

Wata majiya ta ce da sanyin safiyar ranar Laraba, wasu ’yan bindiga da kusan su 10 sun kai hari kauyen Shirigi, inda suka sace iyalan Alhaji Shuaibu Shirigi.

“Da farko sun sace mutum tara amma daga baya mutanen gari suka ceto daya daga cikinsu, sai dai sun harbi mutum daya daga cikinmu a cinya,” a cewar majiyar.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, mun kasa jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar, SP Gambo Isah.