✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun kashe mutane, sun kona gidaje a Taraba

‘Yan bindiga kashe mutane da dama a Kauyen Tunda da ke Karamar Hukumar Bali a Jihar Taraba. Majiyar Aminiya ta ce ana zargin maharan ‘yan sa kai…

‘Yan bindiga kashe mutane da dama a Kauyen Tunda da ke Karamar Hukumar Bali a Jihar Taraba.

Majiyar Aminiya ta ce ana zargin maharan ‘yan sa kai ne, lamarin da ya sa fargabar yaduwar matsalar zuwa Mazabar Taraba ta Tsakiya a jihar.

Maharan da suka hallaka mutane da dama suka kuma kona gidaje kafin su tsere ‘yan kabilar Jukun ne.

Majiyarmu ta ce ana zargin harin Tunga ramuwar gayya ce kan kashe wani Fasto dan kabilar ta Jukun da matarsa da aka yi a Marabar Donga ranar Litinin.

Ta kara da cewa ‘yan kabilar Tiv musamman mata da kananan yara na yin kaura daga yankin domin guje wa sabbin hare-hare.

Tibabe na zaune lafiya a Taraba ta Tsakiya, amma harin na ranar Juma’a ya sanya fargaba a zukatan ‘yan kabilar da ke kauyukan yankin.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Taraba DSP David Misal ya tabbatar da mutuwar mutum biyar a harin.

“Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Taraba ya ba da umurnin tura jami’an rundunar zuwa yankin da abin ya faru da zummar gano wadanda suka aikata laifin”, inji shi.