Akalla mutum biyar mutu a wani farmaki da ‘yan bindiga suka kai kauyen Dawusu da ke Karamar Hukumar Toto, a Jihar Nasarawa.
Mutanen garin sun shaida wa wakilinmu cewar maharan sun kuma kona gidaje da dama.
Salihu Sa’id, wanda harin ya rutsa da shi ya ce mayakan su shigo kauyen ne a daren Litinin bayan mutane sun kwanta barci.
Ya ce daga cikin mutum biyar da ‘yan bindigar suka kashe har da wata matar aure, “sun kuma kona gidaje da dama”
Sa’id ya ce ‘yan bindigar sun rika yin kabbara, suna sarar mutane daga karshe suka shiga gulbi suka tsere.
Mai Martaba Ohimegye na Umaisha-Opanda, Alhaji Abdullahi Usman, ya tabbatar da kisan mutanen biyar ta wayar tarho, ya ce an kai gawarwakin fadarsa da yamma.
“An kawo mani gawa hudu, a nan muka yi jana’izarsu. Sai ‘yan banga suka kara ganin gawar mutum daya a daji.”
Ya kuma nuna rashin jin dadin yadda ake yawaita kai wa mutanensa hari, inda ya kara da cewa “a makon da ya wuce, an yi garkuwa da mutanena 2 kan hanyarsu ta zuwa gona, kuma har yanzu ba a sako su ba”
Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda na Jihar, ASP Ramhan Nansel, ya ce ya yi kokarin yin magana da DPO mai kula da yankin domin jin gaskiyar lamarin amma hakan bai yiwu ba.