✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutane 9 sun sace wasu a Katsina

Wani dan sanda na daga cikin mutanen da aka kashe, sannan ba a iya tantance adadin waɗanda aka yi garkuwa da su ba

’Yan bindiga sun kashe dan sanda da fararen hula takwas tare da yin  garkuwa da mutane da dama a garin Danmusa da ke Jihar Katsina.

A daren Lahadi ne dandazon maharan suka kutsa garin suna harbi kan mai uwa da wabi.

Wani mazaunin garin ya shaida wakilinmu cewa har yanzu ba a iya tantance yawan mutanen da aka yi garkuwa da su ba.