✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe miji da matarsa a Benuwai

Wasu ’yan bindiga sun kashe wani miji da matarsa a yankin Mbabai da ke Karamar Hukumar Guma ta Jihar Benuwai. Wakilinmu ya ruwaito cewa, maharan…

Wasu ’yan bindiga sun kashe wani miji da matarsa a yankin Mbabai da ke Karamar Hukumar Guma ta Jihar Benuwai.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, maharan sun kashe mutumin ne da matarsa yayin da suke dawo da gona da yammacin ranar Talata haye a kan babur.

Mashawarci na musamman kan harkokin tsaro ga gwamnan jihar, Kanal Paul Hemba, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin ganawarsa da manema labarai a ranar Laraba.

Kanal Hemba ya ce, maharan sun yi wa mijin da matarsa dirar mikiya ne yayin da suka kan hanyarsu ta dawowa daga gona inda suka kashe su nan take.

Ya kara da cewa, tuni ’yan uwan wadanda lamarin ya ritsa da su suka fara shirye-shiryen jana’iza tare da cewa wannan hari na daya daya daga cikin gomman wadanda ke aukuwa a yankin.

Sai dai yayin da ake nemi jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Catherine Anene, ta ce ba ta da masaniya a kan aukuwar lamarin.