✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mai ciki sun dauke mijinta a Kaduna

’Yan bindiga sun kashe wata mata mai tsohon ciki suka yi garkuwa da mijinta a Kaduna

’Yan bindiga sun hallaka wata mata mai juna biyu suka kuma yi garkuwa da mijinta a Jihar Kaduna.

Wani shaida ya tabbatar wa Aminiya a ranar Laraba cewa masu garkuwar sun binidige matar ne da yammacin Tatala bayan sun dauke su a gidansu da ke unguwar Rigachikun.

“Masu garkuwar sun kutsa gidan mutanen ne suka yi awon gaba da su kafin daga baya jami’an tsaro suka bi su”, inji shi.

Ya ce an harbi matar ce a lokacin da jami’an tsaro ke musayar wuta da ’yan bindigar da nufin kwato wadanda aka yi garkuwan da su.

“A musayar wutar da suka yi da jami’an tsaro ne masu garkuwar suka harbi matar wadda daga baya ta rasu a asibiti”, amma ’yan bindigar sun tafi da mijin matar.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto dai babu cikakken bayani game da abin da ya wakana, amma shaidan ya ce, “matar da aka kashe tana da tsohon ciki kuma tuni aka yi mata jana’iza bisa tsarin addinin Islama”.

Aminiya ta tuntubi mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Kaduna, Muhammad Jagile, domin karin haske amma bai kai ga yi mata bayani ba.