Mafarauta 18 sun rasu a musayar wuta da ’yan bindiga a kusa da garin Maihula a Karamar Hukumar Bali a Jihar Taraba.
’Yan bindiga kimanin 200 sun yi kokarin kutsawa garin Bali, hedikwatar karamar hukumar, amma mafarauta suka hana su a ranar Talata.
Basaraken yankin, Kur Bali, Mahamud Abubakar, ya shaida mana cewa mafarauta sun yin nasarar dakile harin da ’yan bindiga suka kawo wa yankinsa.
Shaidu sun ce maharan da ke dauke da muggan makamai sun kashe 15 daga cikin mafarautan, suka jikkata wasu da dama.
- An tsinci gawar mutumin da aka sace tare da Hakimin Kaduna
- Dan sandan ya harbi mutane a cikin Keke NAPEP a Kaduna
Da yake tabbatar da hakan, shugaban kungiyar mafarauta a karama hukumar, Adamu Dantala, ya ce ’yan bindigar sun yi wa wasu mutanensa kwanton bauna a kusa da garin Dakka, suka kashe mafarauta uku.
Ya roki, “gwamnati ta samar mana da makamai da tallafin kula da iyalan wadanda suka rasu da kuma jinyar wadanda suka jikkata.”
Kakakin ’yan sanda jihar Taraba, SP Usman Abdullah bai amsa kiran waya ko rubutaccen sakon da wakilinmu ya tura masa na neman bayani kan lamarin ba.