✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun kashe limami da dagachi a rikicin kabilanci

‘Yan bindiga sun kashe Dagachi da Limamin garin Bagoni da wasu mutum uku. Dukkan mamatan ‘yan bindigar suka kashe ‘yan kabilar Jibawa ne a Karamar…

‘Yan bindiga sun kashe Dagachi da Limamin garin Bagoni da wasu mutum uku.

Dukkan mamatan ‘yan bindigar suka kashe ‘yan kabilar Jibawa ne a Karamar Hukumar Bali a Jihar Taraba.

‘Yan kabilar wadanda wani bangare ne na kabilan Jukun na zargin yan kabilan Tibi da Kai harin.

Rahotanni sun ce ‘yan bindiga sun kashe wasu mutum huku a wani hari da suka kai garin Wurbo.

Wani wanda ya sha sha da kyar daga harin ya ce maharan sun kona gidaje masu yawan gaske a garuruwan biyu.

Ya shaida wa Aminiya cewa su ma mazauna garin na Wurbo Jibawa ne.

A halin da ake ciki matasan kabilar sun na kurarin daukar fansa a kan Tibaben da ke zaune yankin.

Wakilin Aminiya ya jiyo cewa daruruwan ‘yan kabilan Tibi na kaurace wa kauyukansu saboda gudun kawo masu hari.

Rikicin kabilanci tsakanin kabilun Tibi da Jukun ya yi sanadiyyar kashe mutane da dama a kananan hukumomin Donga da Wukari da Bali.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Taraba DSP David Misal ya ce mutum biyar ne aka kashe a harin.

DSP David Misal ya kuma ce an tura karin yansanda zuwa yankin domin tabbatar da zaman lafiya.