Wasu ’yan bindiga sun kai mamaya kauyen Kawaran Rafi da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, inda suka kashe babban Limamin garin, Dan Liman Isah.
Aminiya ta samu cewa maharan sun kai wa marigayin takakka ne har gida a yayin da suka yi wa garin dirar mikiya, inda suka harbe shi nan take bai ko shura ba kuma suka kama gabansu ba tare da dibar wata dukiya ko satar wasu mutanen ba.
Ana ganin cewa kisan gillar da aka yi wa malamin na da nasaba ne da da’awarsa ta bayyana tsagwaran adawa a kan yadda ’yan bindiga ke faman cin karensu babu babbaka wajen aikata ta’addanci na kashe-kashe da garkuwa da mutane a yankin.
Haka kuma, masu garkuwa da mutane sun kashe Sarkin Yakin garin Godogodo, Mista Yohanna Abu.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da faruwar lamuran biyu da suka auku a lokuta daban-daban.
Ya ce an sanar da jami’an tsaro game da lamarin domin daukar matakin da ya dace.
A cewarsa, ’yan bindigar sun kai hari kauyen Nisama da ke Karamar Hukumar Jema’a a daren ranar Juma’a, inda suka yi awon gaba da Mista Abu da kuma wani mazaunin garin, Mista Charles Audu.
Kwamishinan ya ce a kokarin da Mista Abu ya yi na tsere wa daga hannun maharan ne suka harbe shi nan take.
Mista Aruwan ya ce ya zuwa yanzu wasu mutum biyar sun shiga hannu wadanda ake zargi, a yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da tsananta bincike.
Ya kara da cewa, Gwamna Malam Nasir El-Rufa’i ya bayyana bakin cikinsa dangane da lamuran biyu da suka faru, inda ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya tare da mika sakon ta’aziya ga ’yan uwan wadanda harin ya ritsa da su.