Hukumar Kiyaye Afkuwar Hadurra ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar jami’anta guda biyu ranar Litinin a garin Mararaban Udege da ke jihar Nasarawa.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, ACM Bisi Kazeem wanda ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ya kuma ce ’yan bindigar sun kuma sace wasu jami’an guda 10 a yankin.
Bisi ya ci gaba da cewa an kai wa jami’an su 26 da suka fito daga shiyyoyin jihohin Sakkwato da Kebbi harin ne a kan hanyarsu ta zuwa makarantar FRSC da ke Udi.
Ya ce, “’Yan bindiga da masu garkuwa da mutane ne suka kai musu hari a daidai mahadar Udege, kan hanyar Maraban-Udege a Jihar Nasarawa ranar Litinin da misalin karfe takwas na safe.
“Jami’an da yawansu ya kai 26 na cikin tafiya a manyan motoci ne guda biyu lokacin da aka kai musu harin.
“Nan take daya daga cikin jami’anmu da ke cikin motocin ya mutu, yayin da wani kuma ya mutu a asibiti, wasu mutum shida kuma suka samu raunuka.
“Takwas daga cikinsu sun samu kubuta ba tare da ko kwarzane ba, yayin da kusan mutum goma da ba a gan su ba ake zargin an yi garkuwa da su”, inji sanarwar.
Tuni dai Shugaban FRSC na kasa, Dokta Boboye Oyeyemi ya sanar da hukumomin da suka kamata don ganin an yi bincike da nufin kubutar da wadanda aka sace din da kuma cafke ’yan bindigar.
Ya kuma yi kira ga dukkannin ma’aikatan hukumar da kada lamarin ya sanyaya musu gwiwa a kan aikin nasu, yana mai ba su tabbacin cewa hukumar da sauran hukumomin tsaro za su tabbatar an cafke ’yan bindigar da kuma kubutar da wadanda aka kama.