✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe gomman mutane a Katsina

An kashe wasu fasinjoji biyar ciki har da direban motar mai suna Ɗan Mashi.

Aƙalla mutum 17 ne aka ce an kashe a wasu hare-haren ‘yan bindiga a wasu ƙauyukan Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara ta Jihar Katsina.

Lamarin na baya-bayan nan wanda ya faru a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ya shafi wata motar fasinja da ‘yan bindiga suka kai wa hari a kusa da ƙauyen Ɗan Marke da ke kan titin Ƙanƙara zuwa Marabar Ƙanƙara yayin da take dawowa daga kasuwa.

Wani mazaunin garin ya shaida wa wakilinmu cewa, an kashe mutum biyar a nan take, ciki har da direban motar mai suna Ɗan Mashi, yayin da wasu da suka samu raunukan na harbin bindiga ke karɓar magani a asibiti.

Ya ƙara da cewa, an sace biyu daga cikin fasinjojin, ciki har da ɗan direban da ya mutu.

Har ila yau, a safiyar ranar Alhamis, an ce an kashe manoma bakwai a gonakinsu a ƙauyen Katsalle da ke kusa da Mabai a Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara.

Wani mazaunin garin da ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce a farkon makon nan ‘yan bindigar sun kuma kashe wasu manoma uku a gonakinsu yayin da suka sha alwashin ba za su bari manoman su yi noma a wannan daminar ba.

“Duk waɗannan wuraren gonaki ne da ke kusa da ƙauyukan. Mun daɗe da barin gonakinmu da ke nesa da ƙauyukanmu saboda fargabar harin.

“Sai dai abin takaici ne yadda suke ci gaba da kashe mutane a yanzu da sace wasu don neman kuɗin fansa,” inji shi.