✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe fiye da mutum 50 a Zamfara

Ba don daukin da jami'an tsaro suka kawo ba da abin sai ya wuce haka.

Kimanin mutum 56 ne suka rasa rayukansu yayin da ’yan bindiga suka hari wasu kauyuka uku a Karamar Hukumar Bakura ta Jihar Zamfara.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa harin ya auku ne a ranar Juma’ar da ta gabata.

“Muna tsaye a tsakiyar garin Damrisai kawai muka hangi mutane sun doso mu da gudun tsiya.

“Kafin mu ankara kuwa sai muka rika jin rugugin harsashi ta ko-ina.

“Daga nan sai muma muka arce.

“Allah dai ya yi nuna da sauran kwanaki a duniya, amma da tuni mun zama gawa,” a cewar wani tsohon Kansila da ya bukaci a sakaya sunansa.

Ya ce ’yan bindigar sun afka wa kauyukan Sabon Garin Damri, Damri da Kalahe da karfe biyun rana yayin da aka sakko daga sallar Juma’a kuma mutane sun ci gaba da shagulgulan sallah kamar yadda suka saba.

Wani mazaunin Damri mai suna Mu’azu Damri ya shaida cewa ba don daukin da jami’an tsaro suka kawo ba da adadin wadanda rayukansu za su salwanta sai sun wuce wanda aka samu a yanzu.

Ya ce, “mafi yawa daga cikin wadanda maharan suka kashe baki ne da daga kauyukan dake kurkusa da wadannan garuruwa.

“Sai dai kuma zan yaba wa jami’an tsaro bisa kokarin da su ka yi na fatattakar ’yan bindigar daga garin Damri.

“Da jami’an tsaro suka bude wa ’yan bindigar wuta ne aka samu saukin abin.

“Da wuta ta yi wuta fa hatta abinci da dabbobin da suka sace na jama’a duk sun watsar dasu suka arce.