Rahotanni sun bayyana cewa wasu ’yan bindiga sun kashe wani Fasto a yankin Aloko- Oganenigwu na Karamar Hukumar Dekina ta Jihar Kogi, mai suna Jacob Wodi Hulobu.
An ce Faston ya tsere ne tare da wasu mambobinsa zuwa wani wuri lokacin da maharan suka kai farmaki a lokacin da suke tsaka da ibada da safiyar ranar Lahadi.
- Dan jaridar da aka kora saboda caccakar Gwamnan Borno ya sami aiki a Turkiyya
- An tsinci gawar mai ciki a gefen titi a Kano
A cewar daya daga cikin mambobinsa Samuel, Faston ya koma cocin ne domin duba halin da ta ke ciki bayan harin da maharan suka kai.
“Ya tsere yayin da ake ibada a coci da safe. Ya yi tunanin komai ya lafa ne, shi ne ya sake komawa ya duba halin da cocin ke ciki wanda a nan suka same shi suka kashe shi,” in ji Samuel.
Aminiya ta samu labarin cewa Fasto din wanda a baya ya wallafa a shafinsa na Facebook kan yadda ya tsallake rijiya da baya a harin da aka kai da safiyar ranar, ya mutu bayan sa’o’i kadan.
An ruwaito cewar Hulobu ya shirya wani taron addu’a na musamman da zai gudana tsakanin ranakun 13 zuwa 15 ga watan Afrilu a cocin kafin afkuwar lamarin.
Ya rasu ya bar matarsa da yaro daya.