Wasu ’yan bindiga sun kashe baturen ’yan sanda (DPO) na yankin Paiko, hedkwatar Karamar Hukumar Paikoro da ke Jihar Neja, SP Mukhtar Sabi’u, tare da wasu jami’an ’yan sanda su hudu.
Jami’an tsaron sun gamu da ajalinsu ne a kauyen Kwakuti da ke kan hanyar Minna zuwa Suleja a Jihar, ranar Asabar.
- Gwamnan Yobe ya bude sabuwar kasuwar Nguru mai shaguna sama da 500
- An min tayin miliyan 150 da mota don na koma tafiyar Tinubu amma na ki — Sarkin Waka
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar, DSP Wasiu Abiodun ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu.
Ya ce mutanen sun mutu ne yayin musayar wutar da suka yi da ’yan bindigar, yayin da su ma suka samu nasarar kashe wasu daga cikin maharan.
Wasiu ya ce, “Wajen misalin karfe 11:00 na rana, mun sami rahoton cewa an hangi ’yan bindiga a wajen kauyen Kwakuti da Dajibge da Lambata, a kokarinsu na zuwa su kashe wasu mutane a wasu kauyuka da ke yankin Karamar Hukumar Gurara ta Jihar.
“Gamayyar jami’anmu de ke yankin Gawu-Babbangida da na Paiko da sojoji da ’yan sa-kai sun bazama wajen, inda nan take aka fara musayar wuta, aka kashe wasu daga cikin maharan, wasu kuma suka gudu da raunuka a jikinsu,” in ji shi.
Wani direba da ke bin hanyar Minna zuwa Abuja ya shaida wa Aminiya cewa maharan masu tarin yawa sun tare hanyar ne wajen misalin karfe 10 na safiyar Asabar na tsawon sa’o’i. lamarin da ya tilasta wa matafiya da dama juyawa.
Ya ce, “Jiya [Asabar] a tashoshin motarmu na Minna da kuma Jabi a Abuja, an fuskanci karancin fasinjoji saboda abin da ya faru. Galibinsu sun rika komawa gida daga tashoshin bayan jin labarin abin da ya faru, wajen misalin karfe 1:00 na rana.
“Wasu daga cikin abokan aikinmu da lamarin ya ritsa da su a kan hanya sun ce sun ga maharan masu yawan gaske a kusa da kauyen Kwakuti da daruruwan shanu. Dole suka dawo Minna, wanda a sakamakon haka kuma, fasinjoji da dama sun fasa tafiyar. Idan da ka je tasahr Jabi jiya, za ka iske babu fasinjoji sosai.”
Aminiya ta kuma gano cewa maharan sun yi kokarin kai farmaki kasuwar Chibani da ke Karamar Hukumar Munya a ranar Juma’a, amma ayarin jami’an tsaro suka dakile su.
Wani mazaunin yankin da bai amince a ambaci sunansa ba ya ce maharan sun kuma kai farmaki kauyen Zazzaga, shi ma da ke Karamar Hukumar ta Munya, inda suka firgita mutanen da ke cin kasuwar mako-mako a Mutum Daya.