✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

‘Yan bindiga sun kashe dakarun soji 11 a Kaduna

Maharan sun kai farmaki sansanin dakarun sojin da ke Birnin Gwari.

Akalla dakarun soji 11 ne suka rasa rayukansu yayin wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai kan wani sansanin sojoji da ke Karamar Hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

‘Yan bindigan sun isa sansanin ne da ke kusa da kauyen Polwire a ranar Litinin, sannan sun dauki wani lokaci suna musayar wuta da  dakarun sojin.

Wata majiya daga rundunar soji Najeriya ta ce ‘yan bindigar sun isa sansanin ne akan babura dauke da muggan makamai.

Majiyar ta ce an shafe sa’a biyu ana gwabzawa tsakanin ‘yan bindigar da dakarun soji da ke sansanin.

“Mun rasa sojoji 11 kuma an raunata 19 a yayin harin. Maharan sun kuma kona wasu motoci masu sulke uku bayan da suka mamaye sansanin”, cewar wani soja.

Majiyar ta kuma ce maharan sun kwashe makamai masu yawa daga sansanin.

An kai sojojin da aka raunata zuwa babban asibitin Birnin Gwari da asibitin sojojin sama, yayin da aka kai gawarwakin wadanda suka mutu zuwa asibitin 44 da ke cikin birnin Kaduna.

Sai dai ba a sami jin ta bakin kakakin rundunar sojin Najeriya, Onyema Nwachukwu ba, kan halin da ake ciki a yankin na Birnin Gwari kan harin da ‘yan bindigar suka kai kan dakarun sojin.