Wasu ’yan bindiga sun kashe akalla mutum 20, ciki har da Dagaci a garin Ganar Kiyawa da ke gundumar Adabka a Karamar Hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara.
Aminiya ta gano cewa an kai harin ne ranar Lahadi, kuma yankin ya sha fama da makamantan wadannan hare-haren a baya.
- Tsohon kakakin Ganduje, Salihu Yakasai, ya fice daga APC
- Jirgin sama dauke da mutum 132 ya yi hatsari a China
A baya dai ’yan bindigar sai da suka tilasta wa mutanen yankin biyan Naira miliyan biyu kafin su kyale su su girbe amfanin gonarsu, sannan daga bisani suka sake biyan wata miliyan biyun don karbo wasu mutum biyu da aka sace.
Mazauna yankin sun ce mutanen da ke dauke da makamai a kan babura dai sun farmake su ne lokacin da suke kan hanyarsu ta wucewa, inda suka sace dabbobi a wani kauyen na daban kuma.
Wani mazaunin yankin mai suna Saminu Usman, ya shaida wa wakilinmu cewa, “Lokacin da suka kawo harin, mutane sun rika guduwa don tsira da rayukansu, amma sai suka fara bin su a kan babura suna harbewa.
“Sun kashe akalla mutum 19, ciki har da Dagaci. Bayan haka, sai suka fantsama cikin daji, mutane kuma suka fara debo gawarwakin ’yan uwansu da aka kashe don yi musu jana’iza.
“Daga nan sai maharan suka dawo makabarta suna tunanin ko an fara yi musu jana’iza, amma suka tarar ba kowa, sai suka koma cikin daji.
“Daga bisani an kai mutanen gundumar Adabka mai nisan kilomita uku daga garin da aka kai harin, inda aka yi musu jana’iza a fadar Hakimin yankin,” inji Saminu Usman.
Majiyar ta ce mutanen da suka rika guduwa, yawancinsu mata da kananan yara ne, sun tafi garin Adabka, don neman mafaka.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, duk yunkurin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Muhammad Shehu, ya ci tura.