’Yan bindiga sun kashe wani sabon ango, sun kuma yi awon gaba da amaryasa bayan kwanaki 11 da ɗaura aurensu a wata unguwa a Jihar Nasarawa.
Ganau sun shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun kai hari gidan sabbin ma’auratan ne da misalin ƙarfe karfe 11:00 na dare ranar Laraba, inda suka harbe angon har lahira, sannan suka tafi da matar zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Akaleku, da ke Ƙaramar Hukumar Obi ta Jihar Nasarawa, a kan hanyar Lafia zuwa Makurɗi.
Ma’auratan, Mista da Misisi Alu Anzaku, an ɗaura aurensu ne a ranar 12 ga Afrilu, 2025.
- An kama mata 2 na ƙoƙarin sayar da ƙananan yara da aka sace
- An kori lakcara kan neman lalata da ɗaliba matar aure
Majiyoyi masu kusanci da iyalan ma’auratan sun ce da alama suna cikin lokacin amarci lokacin da wannan mummunan lamari ya faru, wanda ya katse sabuwar rayuwarsu tare.
Har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto, ’yan uwa da abokan arziki sun ci gaba da nuna matukar damuwa, saboda har yanzu ba a samu wani labari game da inda amaryar da aka sace take ba, ko kuma halin da take ciki.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa ba amsa kiran waya da sakonnin tambayoyin da wakilimmu ya aika mata game da lamarin ba har zuwa lokacin da aka kammala rubuta wannan labarin.