✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe Ahmed Gulak

’Yan bindiga sun harbe tsohon hadimin tsohon shugaban kasa a hanyarsa ta zuwa Abuja.

’Yan bindiga sun kashe Ahmed Gulak, tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa kuma tsohon Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Siyasa, a zamanin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan.

Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun harbe Barista Ahmed Gulak, a Owerri, Jihar Imo, ranar Asabar da dare, a hanyarsa ta komawa Abuja daga Jihar Imo.

Dokta Umar Ardo, fitaccen dan siyasa kuma jigo a Jihar Adamawa, inda Gulak ya fito,  ya ce, “Na samu labarin rasuwar dan uwa, aboki kuma abokin karatuna, Barista Ahmed Gulak, wanda ’yan bindiga suka kashe shi a Owerri, Jihar Imo.

“Allah Ya gafarta masa, Ya karbi ayyukansa nagari, Ya kuma rahamshe shi; Allah Ya ba wa iyalansa hakurin rashi, idan kuma lokacinmu ya yi, Allah Ya sa mu yi kyakkyawan karshe,” kamar yaddda ya wallafa shafinsa Facebook.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani daga hukumomi game da rasuwar fitaccen dan siyasan dan asalin Jihar Adamawa.

Wasu bayanai sun ce, an kashe shi ne a yankin Obiangwu na Jihar Imo, a hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama da nufin komawa Abuja.

Gulak shi ne jami’in jam’iyyar APC da ya gudanar da zaben fidda dan takarar gwamnan jam’iyyar mai cike da rudani a Jihar Imo, wanda Sanata Hope Uzodinma ya lashe a 2019.

Kafin sauya shekarsa zuwa jam’iyyar APC a 2018, Gulak ya kasance tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Adamawa.

A zamanin mulkin na PDP, ya taba zama hadimi ga tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Muhammad Namadi Sambo.