Azal ta afka wa kungiyoyin wasu ’yan bindiga biyu a Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna, inda suka kashe mutum tara a tsakaninsu.
Binciken sirri na jami’an tsaro ya gano yadda lamarin ya faru sannan suka sanar da gwamnatin jihar Kaduna halin da ake ciki.
- An yi gasar jiragen alfarma a Kano yayin auren Yusuf Buhari
- Ba mu amince da dakatar da Abba Kyari ba —Sheikh Jingir
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa.
A cewarsa, wani kasurgumin dan bindiga da ake wa lakabi da ‘Godon Mota’ ne a ranar Laraba ya jagoranci yaransa suka kai farmaki kauyen Garke inda suka yi artabu da wata kungiyar ’yan bindiga wanda hakan ya yi sanadin mutuwar mutum tara a cikinsu.
Aruwan, ya bayyana cewa ba a san abin da ya jawo rikicin a tsakaninsu ba ba, amma alamu sun nuna cewa sun samu sabani ne kan rabon kudin fansar da suka karba.
“Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Hadiza Balarabe, ta karbi rahoton faruwar lamarin, inda ta sake umartar jami’an tsaro da su zage damtse wajen yakar bata-gari a jihar,” a cewarsa.
Ya kara da cewar jami’an tsaro na ci gaba da bincike kan lamarin tare da tsaurara matakan tsaro.