’Yan bindiga sun sako karin wasu mutum bakwai daga cikin fasinjojin da suka yi garkuwa da su a harin da suka kai wa wani jirgin kasa da ke jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja a ranar 28 ga watan Maris na bana.
Wannan dai na zuwa ne bayan shafe kusan watanni uku a hannun wadanda suka yi garkuwa da su, inda mutum bakwai da su ka hada da maza shida da mace daya suka shaki iskar ’yanci a ranar Asabar.
- Shugaban Sri Lanka Gotabaya Rajapaksa zai yi murabus
- Ya nemi agolansa ya biya diyyar rainonsa da ya yi
Jaridar Leadership ta ruwito cewa, wani hadimin Sheikh Dokta Ahmad Abubakar Gumi, Malam Tukur Mamu (Dan-Iyan) Fika) ne ya shiga tsakani har aka kai ga sake sakin wasu bakwai daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su.
Wadanda aka saki a yanzu sun hada da Bosede Olurotimi, Abubakar Zubairu, Alhassan Sule, Sadiq Ango Abdullahi, Muhammad Daiyabu Paki, Aliyu Usman da kuma wani dan kasar waje daya tilo dan asalin kasar Pakistan, Dokta Muhammad Abuzar Afzal.
Mamu ya ce nasarar da aka samu a yanzu na da nasaba ne shiga tsakani da sulhu da Sheikh Dr. Ahmad Gumi ke yi da ’yan bindigar.
Ana iya tuna cewa, a ranar 11 ga watan Yunin da ya gabata ne ’yan bindigar sun sako wasu mutum 11 da suka hada da mata shida da maza biyar daga cikin fasinjojin 62 da suka yi garkuwa da su.