✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe, sun sace ’yan yawon Sallah a Katsina

’Yan bindiga sun kashe dan yawon Sallah sun sace wasu a Jibiya

’Yan bindiga sun kai hari kan wasu ’yan yawon Sallah suka kashe daya daga cikinsu tare da yin garkuwa da wasu biyu a Jihar Katsina.

’Yan bindigar sun kai wa ’yan yawon Sallan da ke hanyarsu ta dawowa daga Katsina hari ne a Karamar Hukumar Jibiya ta Jihar Katsina.

’Yan yawon sallan sun yi mugun gamon ne a wani shingen tare ababen hawa da bata-garin suka kafa a kan hanyar.

Matashin da ’yan bindigar suka kashe, Anas Adamu, dalibin ajin karshe ne a Kwalejin Ilimi da ke Katsina.

Wani abokin mamacin, Muhammad Aliyu, ya ce bayan ’yan bindigar sun kafa shingen a cikin dare ne motocin matasan suka kutsa cikinsu a bisa kuskure.

“Bayan bukukuwan Sallah suka baro Katsina da misalin 8:30 na dare zuwa Jibiya.

“A hanya, sai motar da ke gaba ta ga shingen a kurkusa ta fada ciki, amma direban ya yi sa’a, ya sake dawo da motar kan titi, suka tsere.

“Mota ta biyu da ta uku kuma ’yan bindigar sun riga sun far musu, suka harbi daya direban a kafa suka yi kokarin sace sauran mutum biyu da ke cikin motar

“Shi kuma mamacin ya yi kokarin tserewa amma suka kama shi suka rika saran shi, suka karya mishi hannu da kafa sannan suka cinna mishi wuta, a haka ya rasu.”

Mun tuntubi kakakin ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, amma ya ce ba shi da labari.

Sai dai ya ce zai tuntubi DPO na yankin Jibiya domin samun bayanai.